News
Gwamnatin Najeriya ta gayyaci shugabannin jami’o’in kasar
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta gayyaci shugabanni da iyayen jam’io’i, tare kuma da shugabannin gudanarwa na jami’o’in gwamnatin tarayya zuwa wani zama da za ta yi da su game da batun yajin aikin kungiyar malaman jami’o’in kasar.
Gidan Talabijin na Channels Tv a Najeriya ya ruwaito cewa sanarwar zaman wanda aka shirya yinsa ranar shida ga watan Satumbar 2022, na kunshe ne cikin wata wasika da hukumar gudanarwar jami’o’in kasar (N.U.C) ta aike wa shugabannin a kokarinta na shiga tsakani domin kawo karshen yajin aikin da malaman jami’o’in kasar ke yi.
‘Yan sanda sun kubutar da yara biyu a Zamfara
Sanarwar ta ci gaba da cewa ”kamar yadda iyayen jami’o’i da shugabbanin gudanarwa da kuma shugabannin jami’o’i suka san halin da jami’o’in kasar nan ke ciki na kasancewa a rufe sakamakon yajin aikin malaman jami’o’i tun cikin watan Fabrairu”
”Kun kuma san cewa kungiyar ma’aikatan jami’o’i sun janye nasu yajin aikin tun ranar 24 ga watan Agusta , amma kuma ita kungiyar ASUU har yanzu ana dakon matsayinta” kamar yadda yake kunshe cikin wasikar da NUC ta aike wa shugabannin jami’o’in.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
