Connect with us

News

Hukumar kashe gobara ta Kano ta ceci rayuka 91, dukiya ta N24. 9m a watan Agusta

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

 

 

Advertisement

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce ta ceci rayuka da dukiyoyi 91 da kudinsu ya kai Naira miliyan 24.9 daga aukuwar gobara 29 a watan Agusta.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Saminu Abdullahi ya fitar ranar Juma’a a Kano.

An tsare mawaƙi Ice Prince bisa zargin guduwa da ɗan sanda

Mista Abdullahi, ya ce mutane 11 ne suka rasa rayukansu yayin da gobara ta lalata dukiya ta Naira miliyan 8.3 a tsawon lokacin da ake bitar.

 

Advertisement

Ya ce ma’aikatar ta amsa kiraye-kirayen ceto 55 da kuma kararrawar karya 14 daga mazauna jihar.

 

Kakakin ya bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen gudanar da ayyukan da suka shafi gobara domin hana afkuwar hadura.

 

Ya kuma gargadi masu ababen hawa da su rika tukin mota tare da kula sosai domin gujewa hadurra musamman a lokacin damina.

 

Advertisement

 

DAILY NIGERIAN

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending