Connect with us

Sports

Gasar Premier: Manchester United ta doke Arsenal 3-1

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADINNI

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Manchester United ta doke Arsenal 3-1 a wasan mako na shida a gasar Premier League da suka buga ranar Lahadi a Old Trafford.

Advertisement

United ta fara cin kwallo a minti 35 ta hannun Anthony, sabon dan wasan da ta dauka a bana daga Ajax.

An Dawo Da Littafin Da Aka Sace A Dakin Karatu Bayan Shekara 50

Advertisement

Tun a minti na 12 da take wasa Gabriel Martinelli ya ci Manchester United kwallo, amma aka soke ta cewar an yi wa Eriksen ƙeta kafin a jefa ƙwallon a raga.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Bukayo Saka ya farke kwallon da aka ci Gunners.

Advertisement

Sai dai kuma minti shida tsakani Marcus Rashford ya kara na biyu sannan ya ci na uku da ya sa United ta hada maki umun da take bukata.

Rabon da Rashford ya ci Arsenal kwallo tun ranar da ya fara yi wa United wasa a cikin watan Fabrairun 2016, kafin wasan Lahadi ya fuskanci Gunners sau 13.

Advertisement

Dan wasan Manchester United, Antony – wanda shi ne na 100 daga Brazil da ya koma buga Premier League – shi ne na farko daga kasar matashi da ya ci kwallo a wasansa na farko mai shekara 22 da kwana 192.

United ta ci wasa hudu a jere kenan, bayan da aka doke ta karawa biyu tun farko – sun zama na uku da suka yi wannan bajintar bayan Tottenham a 2011/12 da kuma Arsenal a 2018/19.

Advertisement

Arsenal ta yi rashin nasara a wasan Premier da yawa a Old Traford fiye da sauran kungiyoyi har sau 17 aka zura mata kwallaye 49 – a filin Anfield ne ka zura mata masu yawa 69.

Arsenal ta kasa yin nasara a wasa bakwai baya, idan ta fuskanci Manchester United tana ta daya a kan teburi, ta yi rashin nasara biyar da canjaras biyu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending