News
Ambaliya na barazana ga sama da mutum miliyan 100 a Pakistan
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Hukumomi a Kudancin Pakistan sun umarci mutane kusan 100,000 da su bar gidajensu a kokari da ake na kare su daga ɓallewar wata madatsar ruwa a wani babban tafkin kasar.
Mutane a lardin Sindh na cikin barazana sakamakon shiga gidajensu da ruwa daga kogin Manchar ke yi , inda jami’ai suka ce sun fara ɗaukar matakai domin kare ɗumbin al’ummomi a yankin.
Gasar Premier: Manchester United ta doke Arsenal 3-1
Ba a dai san hakikanin mutanen da za su bar gidajensu ba, inda ake samun kwararar jama’a zuwa tantunan wucin gadi da aka samar.
Pakistan dai na cikin mawuyacin hali bayan mummunar ambaliya ta makonni da ta shafi al’ummomi sama da miliyan 30.
Hukumomi na kuma cikin shirin ko-ta-kwana saboda hasashen samun mamakon ruwan sama a arewacin kasar cikin kwanaki masu zuwa.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
