News
Najeriya da Poland sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Samar da Abinci
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da takwaransa na Poland sun rattaba hannu kan yarjejeniyar magance matsalar karancin abinci da rattaba hannu kan yarjejeniyar magance matsalar karancin abinci a kasar da ma nahiyar Afirka.
Shugaba Muhammadu Buhari da takwaransa na Poland Andrzej Duda ne suka sa hannu kan yarjejeniyar a fadar gwamnatin Najeriya ranar Talata, lokacin ziyarar da Mista Duda ya kawo ziyara.
Mu na ɗaukar mata aiki amma sai wacce ta dace — Kwamandan vigilante na Kano
A ziyarar da ya Mista Duda ya fara ta kwanaki uku a wasu kasashen Afirka, Najeriya ce a sahun gaba, inda suka rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama baya ga ta samar da abinci.
Shugabannin biyu sun kuma tabo batun tsaro da makamashi, inda shugaban na Poland ya kuma bai wa Najeriya tabbacin cewa kasarsa za ta yaukaka huldar kasuwanci lamarin da zai tsaka kan samar da abinci da bunkasa fannin noma.
Sun kuma tattauna kan batun fitar da iskar danyen mai da iskar gas zuwa Poland sa sauran kasashen Turai.
Duda ya amince Najeriya ta na da tarin arzikin albarkatu kasa, ya kara da cewa kasarsa ta na fatan kulla hulda mai dorewa tsakaninta da Najeriyar.
A yau ne ake sa ran Duda zai wuce kasar Ivory Coast, sai kuma ta karshe Senegal a ranar Alhamis, wadda ita ce ta karshe a ziyarar kwanaki ukun da ya ke yi wasu kasashen Afirkar.
