Business
Najeriya za ta ci tarar kamfanonin jiragen sama kan kin saida tikiti da Naira
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin Najeriya ta yi barazanar sanya tara ga kamfanonin jiragen sama na kasashen waje, da suka ki amincewa da sayan tikiti da naira maimakon dalar Amirka.
Ministan sufuri, Hadi Sirika, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a wani bangare na taron majalisar zartaswa da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar gwamnati da ke Abuja.
Napoli ta lallasa Liverpool da ci 4-1 a gasar cin kofin zakarun Turai
Sirika ya kara da cewa, bayanan sirrin da suka samu na cewa wasu daga cikin kamfanonin jiragen saman, sun ki amincewa su karbi Naira, kuma hakan ya sabawa dokokin Najeriya.
Ya kara da cewa, am bai wa ma’aikatar sufurin jirgin sama ta Najeriya umarnin magance matsala irin wannan da daukar mataki kan kamfanonin da suka nemi take doka.
A karshe Sirika ya yi kira u daina amfani da kafafen sda zumunta wajen bayyana bukatun da suke bukata daga gwamnatin Najeriya, maimakon haka su tun kari gwamnati gaba gadi domin bin matakan diflomasiyya wajen magance duk wata matsala.
Rashin dalar Amirka da Najeriya ke fama da karancin ta ya janyo kamfanonin jiragen kasashen waje kamar Emirate mallakin hadaddiyar daular larabawa, dakatar da zuwa kasar.
BBC NEWS
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
