News
Wasu ‘yan Venezuela sun bata bayan hawa wani tsauni yin addu’a
DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAH
Jami’an aikin agaji na can suna ci gaba da neman wasu mutane da suka bata lokacin da suka hau wani tsaunin Andes domin yin addu’a.
An samar da jirage marasa matuki da kuma karnuka zuwa saman tsaunin da ke kusa da garin La Grita na jihar Tachira.
Najeriya za ta ci tarar kamfanonin jiragen sama kan kin saida tikiti da Naira
Wani jami’i a hukumar kare jama’a, ya ce mutanen da ake nema sun kai 16 zuwa 20, amma kafar yada labaran yankin ta ce ta yiwu adadin ya wuce haka.
‘Yan uwan mutanen sun ce ba su ji duriyarsu ba, tun bayan balaguro zuwa tsaunin ranar 22 ga watan Agusta da ya wuce.
Makoftan wurin sun shaidawa jaridar Nación cewa, yawancin mutanen sun tanadi abinci da tantina da tabarmi a lokacin da sukai shirin hawa tsaunin, wanda suka kira kwanaki hudu na yin addu’o’i.
BBC NEWS
