Connect with us

News

Kidayar 2023: Za Mu Kashe N21bn Don Shata Taswirar Najeriya – Osinbajo

Published

on

DAGA YASIR SA ABDULLAH 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira biliyan 21 domin shata taswirar yadda kidayar jama’a ta 2023 za ta gudana.

Advertisement

 

Osinbajo ya kuma ce duk da haka, akwai bukatar karin kayan aiki da karin hanyoyin samun kudi kwarara ga hukumar da ke kula da aikin.

Advertisement

 

Chelsea Ta Tabbatar Da Nadin Graham Potter A Matsayin Sabon Kocinta

Advertisement

Osinbanjo ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja, a taron da Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta shirya, mai taken “Goyon Bayan Tsarin Kidayar Jama’a a Najeriya”.

 

Advertisement

Mataimakin Shugaban Kasar na musmaman a harkokin yada labarai, Laolu Akande, wanda shi ne ya wakilici Osinbajon ya ce gwamnati ta sahale a cire Naira biliyan 198 daga kasafin kudin bana, kuma tuni ta saki kaso 60 cikin 100 na kudin.

 

Advertisement

Ya kuma ce, “Daga nan zuwa 2050, ana sa ran yawan ‘yan Najeriya zai kai miliyan 400, don haka dole ne gwamnati ta ci gaba da bayar da ingantaccen ilimi, da harkar lafiya da kuma abinci.

 

Advertisement

“Haka kuma akwai bukatar inganta bangaren tsaro, da samar da aikin yi ga matasa, wadanda su ne ke da fiye da rabin kason Najeriya.

 

Advertisement

“Don haka kidayar na da muhimmacnci sosai a wannan gaba, kuma shiri na musamman da tattara bayanan da suka kamata abu ne mai muhimmanci sosai, wajen samar da ci gaba mai dorewa da cigaban kasa.

 

Advertisement

A nasa bangaren, shugaban hukumar ta NPC, Nasir Kwarra, ya ce taron ya tattauna batutuwan da suka shafi tafiyar da kidayar a abadi, da kuma shirye-shiryen tunkarar kalubalen da aikin ke tattare da shi

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

DAILY TRUST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending