Connect with us

News

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 3, ta lalata gidaje 1,453 a kananan hukumomin Bauchi 2

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Dr Ibrahim Kabir, Darakta Janar na Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Bauchi (BASEPA) ya tabbatar da mutuwar mutane 3 sakamakon ambaliyar ruwa da ta lalata gidaje 1,453 da gonaki da dama a kananan hukumomin Zaki da Gamawa.

Kabir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Gwamna Bala Mohammed lokacin da ya kai ziyarar jajantawa al’ummar da abin ya shafa a ranar Asabar a karamar hukumar Zaki.

Advertisement

Dalibai Sun Daure Malami Sun Lakada Masa Duka Kan Samun Maki Kadan
Ya ce bayan tantance irin barnar da mamakon ruwan sama ya yi a ranar Laraba, an gano ya kashe mutane 3 da lalata gidaje 1,453 da gonakin da ba a tantance adadinsu ba a kananan hukumomin biyu.

Ya ce ambaliyar ta kuma katse hanyoyin da suka hada kananan hukumomin biyu da al’umma da kuma wasu sassan jihar a wurare 6 a kan babbar hanyar.

Advertisement

“A matsayin matakan kwantar da hankali, al’ummomin suna buƙatar kwale-kwale 14 a matsayin hanyar sufuri don ketare hanyoyin da aka yanke don ci gaba da kasuwancinsu na yau da kullun,” in ji shi.

Dokta Kabir ya shawarci al’ummomin da su koma wuraren da suka fi tsaro domin tabbatar da tsaron lafiyarsu.

Advertisement

Gwamna Mohammed ya jajanta wa al’ummar yankin kan mutuwar mutane uku da lalata gidaje da gonaki a kananan hukumomin Zaki da Gamawa.

Ya yi kira da a hada karfi da karfe wajen magance munanan illolin da ambaliyar ruwa ta addabi al’umma a fadin jihar.

Advertisement

Mohammed, a lokacin da yake duba irin barnar da ambaliyar ta yi, ya ce al’ummomin sun fuskanci hatsarin ambaliya.

Ya kuma bayyana cewa ana samun asarar rayuka da dukiyoyi duk shekara a jihar.

Advertisement

Mohammed ya yabawa Gwamnatin Tarayya da Bankin Duniya kan yadda suke shiga cikin sauran bangarorin ci gaba da ababen more rayuwa.

Sai dai ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta taimaka wa jihar wajen samar da mafita ta din-din-din a kan wannan matsala, tare da samar da agaji ga wadanda abin ya shafa.

Advertisement

Gwamnan ya gabatar da kayan agajin tireloli guda biyu na Masara da magunguna da kayan masarufi ga kananan hukumomin Zaki da Gamawa.

Ya kuma umurci hukumar SEMA da ta gaggauta sayo kwale-kwale guda 14 ga al’ummomin da abin ya shafa tare da yin kididdige barnar da ambaliyar ta yi domin baiwa gwamnati damar daukar matakai na gaba.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

SOLACE BASE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending