Connect with us

Opinion

Rayuwa don birge mutane ba ta da amfani

Published

on

Muhammad Muhammad ZAHRADEEN

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADEEN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Wani abu da yake damun ƴan Afirka, ko in ce Hausawa, shi ne son birge mutanen da suke zama tare da su. Misali, sai mutum ya ce shi sai ya saka kaya ko riƙe waya kala kaza don a kiyaye shi. Mace ta ce sai ta saka gwal, ko ki ce sai an yi farin bikinki iri kaza don a kiyaya,  Tambayata: wa kake wa rayuwarka? Kanka ko wani?

Advertisement

Ambaliya Ta Karya Gadar Da Ta Hada Arewaci Da Kudancin Najeriya A Nasarawa

Turawa suna da matsololi a rayuwa da dama. Amma suna da wata falsafa ta rayuwa wadda idan muka ara, za mu ga natija a tamu rayuwar. Misali, ba su ɗau birge wani a matsayin wani abun zo-ka-gani ba. Suna fifita maslahar rayuwarsu ne kawai. Shi ya sa, ba ruwansu da ƙarya ta saka kaya, mallakar waya ko abin hawa, ko aurar matar kece raini.

Advertisement

Dr. Muhsin Ibrahim yace Lokacin da muka kalli fim ɗin “Wutar Kara” a ajina, wata Bajamushiya ta ce ta yi mamakin ganin gidan Ibrahim Mandawari na fim ɗin. Ta ce ba ta taɓa ganin gida ƙato mai kuma kayan alatu irin sa ba a zahiri. Kuma haka ne. Wallahi in dai muhalli ake magana, garin Kano ya fi Cologne tamfatsa-tamfatsan gidaje – kai har ma da wasu manyan garuruwan Turai.

Gaskiya ya kamata mu daidaita tsarin rayuwarmu. Ɗan’uwa, ƴar’uwa, ku tuna cewar birge wasu ba shi da wani amfani. Ka yi tunani sosai a kan wannan batu. Bayan ka birge, sai me? Abun zai maka tsiro? Duk abin da za ka yi, mutanen nan dai sai sun yi magana, kuma ba za ka birge kowa ba. For God’s sake, live YOUR life.

Advertisement

Allah ya sa mu gane, mu kuma gyara, amin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending