Connect with us

News

Yan Kasashen waje 286 sun samu takarkar shaidar zama ‘yan Nakeriya

Published

on

Advertisements
ads

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba wa wasu ‘yan kasashe waje 286 takardar shaidar zama ‘yan kasa.

Shugaban ya bukace su da su kasance ‘yan kasa nagari.

A yayin da yake mika musu takardar, ya ce” Kun sadaukar da kawunanku ga Najeriya a lokacin da kuka nuna soyayyarku da biyayyarku ga Najeriyar, a yanzu ita ma za ta saka musu.”

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum fiye da 130 cikin wata biyu a Nijar

Shugaban ya yi bayanin cewa daga cikin mutum 286 da aka ba wa takardar shaidar zama ‘yan kasar, 208 daga cikinsu sun karbi takardar da ke nuna cewa daya daga cikin iyayensu ne dan kasar shi ya sa suka zama ‘yan kasa, yayin da 78 kuma aka yi musu rijistar zama ‘yan kasa.

Shugaba Buhari, ya bukace su da su rika bayar da gudunmuwa mai kyau ta yadda za a samu ci gaba a kasar, ya ce a matsayinsu na ‘yan kasa dole ne su kiyaye da dokokin kasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending