News
Kama Tukur Mamu Ba Zai Hana Ceto Sauran Fasinjojin Jirgin Kasa Ba’
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Gwamnatin Najeriya ta ce kama Tukur Mamu, mai shiga tsakanin nan a kokarin sakin fasinjojin jirgin kasan da aka sace, ba zai kawo cikas ga yunkurin da gwamnatin kasar ke yi na kubutar da sauran fasinjojin da suka rage a hannun ‘yan bindiga ba.
Ministan kula da harkokin ‘yan sanda na kasar Mohammed Maigari Dingiyadi ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taron majalisar tsaro ta kasa da aka yi a Abuja ranar Alhamis.
Farashin Kayayyaki Ya Yi Mummunar Tsada Irinta A Farko Cikin Shekaru 17 A Nijeriya
“Ina ganin masu maganar sun san Mamu ne kawai ba su san sauran masu sulhu ba tsakanin hukumomi da ƴan fashin.
Akwai mutane da dama da ke sa baki kuma maganganun suna amfani,” in ji Ministan Tsaron, a hirarsa da BBC bayan kammala taron.
Jami’an ‘yan sandan kasa da kasa ne suka kama Tukur Mamu ranar 7 ga watan Satumba a Masar, sannan kuma aka dawo da shi Najeriya bisa umarnin gwamnatin tarayya inda aka mika shi hannun jami’an ‘yan sandan farin kaya na DSS.
Ya ƙara da cewa “Akwai ƴan uwan mutanen da hukumomin tsaro da ke shiga tsakani a lamarin. Kama Mamu ba zai kawo ƙarshen sulhun ba.”
Dama an saba duk wata ake gabatar da irin wannan taro na tsaro a ƙasar, kuma Dingyaɗi ya ce na wannan karon an yi shi ne don tattauna irin ci gaban da aka samu a kawo karshen matsalolin rashin tsaro a kasar.
Ya ce kuma ga irin bayanan da aka samu daga su shugabannin sassan tsaro na wannan kasar shi ne an samu cikakken ci gaba, “kuma mun gamsu da irin ci gaban da ake samu, kuma shugaban kasa ya yaba wa su shugabannin sassan na tsaro.”
Ministan ya ce an kuma nemi shugabannin tsaron da su ci gaba da wannan kokari da ake yi na kai hari wuraren da ƴan ta’adda ke zaune.
-
News7 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News4 days agoKotu Ta Daure Wani Limamin Masallacin Juma’a Wata 1 Kan Tura Bidiyon Tsaraici Ga Matar Aure A Kano
-
News6 days agoƘalubalen Da Masu Ƙananan Sana’o’i Ke Fuskanta Saboda Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano
