News
Nafi kowanne dan takarar majalisar jaha a Dala chanchanta-SAGIR U BANDERAWO
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon shugaban dalibai na Makarantar Kimiyya da Fasaha ta kano wanda aka fi sani da Banderawo , wanda Kuma shi ne dan takarar majalisar jaha a Dala a jam’iyyar ADP yace duk cikin yan takarar majalisar jaha a karamar hukumar Dala yafi kowannen Yan Dan takara chanchanta
Banderawo ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakilin jaridar indaranka a Kano.
2023: Sha’aban Sharada Zai Ayyana Neman Kujerar Gwamnan Kano a Yau
Banderawo yace a batun wakilcin al’umma ana bukatar mutumin da yake da gogewa ya Kuma san matsalolin al’umma Kuma yasan hanyoyin da zai bi wajen magance matsalolin
Bandirawo Wanda yace wakilci kamar irin na majalisar jaha yana bukatar gogewa sosai wajen aiwatarwa fiye da na.majalisar jahar ” Kuma abatu takarar ana bukatar mutum Mai mutunci, mutum na matasa, mutum mai karrama mutane, ana da bukatar mutumin da shekarunsa suka kai kuma mutum mai Ilimi dai-dai gwargwado, Kuma al’umma suka San shi, to sai ka duba duk cikin Yan takarar da ake da su a Dala waye wanda zai baiwa Sha’aban abun da yake bukata idan ba ni ba”. A cewa Banderawo
Ya ce ya kamata mutane su sani sun dade suna bada gudunmawa a Siyasa ta hanyar wayar da akan mutane su zabi shugabanni da wakilai na gari, don haka yace suka ga dacewar a wannan karon suma su fito su gwada damar da kundin tsarin mulki kasa ya basu da kuma basirar da suke da ita.
Banderawo yace ya yi tanadi na abubuwan da zasu taimaka wajen ciyar da al’ummar dala gaba fiye da yadda suka Saba gani a baya.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
