News
Wani gini ya ruguje a Legas, ana ci gaba da aikin ceto
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Wani gini ya ruguje a kan titin Sonuga, Palm Avenue, a unguwar Mushin a jihar Legas.
Babban Sakatare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, Dakta Olufemi Oke-Osanyinyolu, ya tabbatar wa da wakilinmu faruwar lamarin a ranar Juma’a.
Gwamnatin Kaduna ta nuna damuwa kan cunkoso a hanyar Kaduna-Abuja
Ya ce, “Wani gini ya ruguje a Mushin ‘yan mintoci da suka wuce. Ana ci gaba da aikin ceto.”
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ba a iya tabbatar da cewa wani ya makale a cikin baraguzan ginin da ya ruguje.
Punch
Advertisements
