Connect with us

News

Zakuna sun yi fata-fata da masu ikirarin jihadi a Mozambique

Published

on

Zaki

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Dakarun sojin Mozambique sun ce sun kama wasu masu ikirarin jihadi hudu da ke shigar da mutane cikin kungiyarsu tare da kangarar da su.

Advertisement

Dakarun sojin sun kuma sanar da mutuwar masu ikirarin jihadi 16.

Kwamandan ‘yan sanda Bernardino Rafael ya ce wasu masu ikirarin jihadin sun mutu ne sanadin harbin bindiga a lokacin fafatawa da sojoji, yayin da wasu kuma suka gamu da ajalinsu baya zakuna da kadoji sun auka musu.

Advertisement

Kwamandan ya yi jawani ne a ranar Laraba lokacin da yake ganawa da mazauna yankin Quissanga a lardin Cabo Delgado na arewacin Mozambique.

Bai dai fadi ko ‘yan bindiga nawa ne zakuna da kadojin suka kashe ba, amma dai ya ce ba shakka dabbobin dajin sun ba da gudunmawa wajen mutuwar masu ikirarin jihadi.

Advertisement

BBC

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending