News
Yayin da ASUU ke yajin aiki:Shugaba kasa muhammadu Buhari na shirin karrama ministan Ilimi.
DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAH
A wani lamari da wasu sukai fassara da cin fuska da kuma rashin damuwa da halin da ilimi ke ciki a kasarnan, shugaban kasa, Muhammadu Buhari na shirin karrama ministan Ilimi da kyautar girmamawa.
Ministan Ilimin, Adamu Adamu na cikin wadanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari ke shirin karramawa daga cikin hadiman gwamnatinsa.
Najeriya: Kayayyakin biliyoyin Naira na ci gaba da rubewa a tashohin jiragen ruwa
Kakakin kungiyar daliban jami’ar, NAN Giwa Yisa Temitope ya bayyana cewa hakan cin fuska ne ga daliban Najariya.
Yace hakan ya nuna gwamnati bata damu da watanni 7 da daliban jami’a suka kwashe a gida ba sabida yajin aikin ASUU.
Advertisements
