News
Yan bindiga sun kashe mutum 12 a Jihar Taraba
DAGA KHADIJA ABDULLAH MUHMD
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe akalla mutum 12 a karamar hukumar Bali da ke Jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya.
Lamarin ya faru ne a kauyen Mubizen ranar Lahadi. Ardo Umar Bello, wanda shi ne shugaban kungiyar Dandalin Makiyaya na Jihar Taraba, ya tabbatar wa BBC cewa ‘yan bindigar sun je garin ne sanye da kakin bijilante.
An Haramta Lodin Mutane A Motocin Daukar Dabbobi
Ya ce sun tara mutane a wani waje inda suka gaya musu cewa sun je domin su kama wasu masu laifi ne amma sai kawai suka bude musu wuta inda suka kashe mutum 12.
A cewarsa mutum hamsin ne suka bata bayan sun guje wa harbe-harben ‘yan bindigar, cikinsu har da mata da kananan yara.
Kazalika ‘yan bindigar sun tafi da shanu 130. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Usman Abdulahi, ya tabbatar wa BBC Hausa aukuwar lamarin, sai dai ya kara da cewa sun kama mutum hudu daga cikin ‘yan bindigar.
Tuni dai aka yi jana’izar mutanen da suka mutu.
