Connect with us

News

Yi wa sabbin kungiyoyin jami’a rijista ko a jikinmu – ASUU

Published

on

ASUU na mai da martani kan matakin yi wa wasu kungiyoyi guda biyu rijista ranar Talata

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Kungiyar malaman jai’o’i ta kasa ASUU ta ce yi wa sabbin kungiyoyin kwadago rijista da gwamnati ta yi don malaman jami’a wata shiririta ce kawai, kuma hakan ba zai taba zama barazana ga kungiyar ba.

Mai kudin duniya na kokarin daidaitawa don saye Tuwita

Advertisement

Shugaban kungiyar ASUU na kasa Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da jaridar Vanguard dangane da yi wa sabbin kungiyoyi rijista da ministan kwadago ya yi a ranar Talata.

 

Advertisement

“Ba abin da ya dame mu. Mu kungiya ce mai da’a da alkibla kuma mun san abin da muke yi, da kuma abin da muke nema. Suna iya bai wa dumbin kungiyoyi rijista idan suna so.

 

Advertisement

A ganinmu babu wani tasiri da hakan zai yi. Kuma ba ma jin wata barazana. Kasar Allah tana da fadi!

 

Advertisement

“Mun san wakilanmu, mun san karfinmu kuma mun san abin da muka sa gaba da abin da muke tsinkaye.

 

Advertisement

Wakilanmu ba masu zagon kasa ba ne kuma ba ‘yan kanzagi ba ne.

 

Advertisement

Gwagwarmayarmu ita ce a inganta ilmi a kasar nan. Idan tsarin ya yi kyau, dukkanmu ne za mu ci riba ba kawai ‘ya’yan mambobin kungiyar ASUU ne za su ci gajiyar inganta samar da kudi don harkokin ilmi da ingantattun kayan koyo a jami’o’in ba,” in ji Farfesa Emmanuel

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending