Connect with us

News

NNPP: muna kotu da INEC akan dan takarar Sanata a Kano ta tsakiya — Kwankwaso

Published

on

Kwankwaso

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

 

 

 

 

Advertisement

 

 

 

 

 

 

Advertisement

 

 

Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma dan takarar shugaban ƙasar Nigeria a jam’iyyar NNPP cikin zaɓen shekarar 2023 mai zuwa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace sun shiga kotu tsakaninsu da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, domin basu damar sanya Sanata Rufai Sani Hanga, a matsayin dan takarar Sanata a yankin Kano ta tsakiya, biyo bayan ficewar wanda aka fara bawa takara daga jam’iyyar, wato Sanata Ibrahim Shekarau.

Cikin wata tattaunawa da sashen Hausa na DW, Kwankwaso yace watakila INEC bata fahimta bane, amma har yanzu bisa tsari na doka, ba’a kai lokacin da za’a ce an rufe karbar dan takarar da aka maye gurbi ba, saboda haka ne yasa suka garzaya kotu, domin kotu ta yiwa INEC gyara akan abinda basu fahimta ba, a cewarsa.

Shekarau dai shi ne wanda jam’iyyar NNPP ta zaɓa domin yi mata takarar Sanata a yankin Kano ta tsakiya, daga bisani kuma ya fice daga jam’iyyar bisa zargin rashin adalci, hakan yasa jam’iyyar ta maye gurbinsa da Sanata Hanga, amma kuma a sai sunan Shekarau ya fito a Jadawalin da INEC ta fitar ba sunan Hanga ba.

 

Advertisement

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending