News
Likita ta shawarci ƴan Nijeriya da su rika samun isasshen hutu da guje wa yawan yin aiki
DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAH
Wata likitar yara da lafiyar al’umma a Abuja, Dakta Yashua Alkali-Hamza, ta gargaɗi ƴan Nijeriya da su kiyaye daga salon rayuwa na yin aiki tuƙuru ba tare da hutawa ba.
Ta tabbatar da cewa ƴan Nijeriya za su samu koshin lafiya idan sun saba da al’adar huta wa.
Alkali-Hamza, wadda ita ce babbar jami’a a asibitin kula da kananan yara da jin dadin jama’a, ta bayyana cewa hutu na kara karfin garkuwar jiki da ake bukata domin kawar da cututtuka masu barazana ga rayuwa.
“samin hutu da kuma kwantar da hankali na da mahimmanci ga kowane ɗan adam. Abin da mutane da yawa ba su fahimta ba shine yawancin cututtukan mu su na faruwa ne ta hanyar rashin samun hutu.
“Ba kawai hawan jini ko cututtukan zuciya ba, har ma da waɗanda ake ganin suna haifar da su ta hanyar ƙwayoyin cuta, cututtukan da rashin ƙarfin garkuwar jiki ke haifar wa da sauran cututtuka na yau da kullum.
“Wannan shi ne saboda damuwa na hana jikinmu ya kasance cikin daidaito. Dukanmu mu na da garkuwar jiki da ke bamu kariya da ga shigar cututtuka.
” Lokacin da muke cikin ranshin hutu, wannan tsarin garkuwar jikin na rushewa. Shi ya sa mutane biyu za su iya fuskantar abu ɗaya amma sai ka ga ɗaya ya kamu dayan kuma bai kamu ba,” in ji ta.
Daily Nigerian
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
