News
Ana zaman dar-dar a Mozambique bayan bacewar zaki
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Bacewar wani zaki daga gidan namun daji ya haddasa fargaba ga mazauna yankin gundumar Massingir da ke kudancin Mozambique.
An yi ta ganin zakin a warare daban-daban tun makon da ya gabata a gundumar Massingir da Mabalane mai makwabtaka.
Hisbah ta kama mutane 31 kan zargin karuwanci da shan barasa
Mazauna yankunan sun ce suna cikin fargaba, yayin da zakin ya kashe wasu shanu a yankunan.
Tuni dai aka tura tawagar jami’an gandun daji da ‘yan sanda domin farauto dabbar.
Babban shugaban yankin Zulo Benito Thomisssene ya shawarci mazauna yankin da su rika tafiya a kungiyance a wani mataki na kare kai daga farmakin Zaki.
BBC
Advertisements
