News
Mutum 440 Cikin Wadanda Buhari Ya Ba Wa Lambar Yabo Ya Kamata Suna Gidan Yari a cewar Buba Galadima.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tsohon na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari, Buba Galadima ya soki lambar yabo ta kasa da shugaban kasa ya bawa wasu mutane a baya-bayan nan.
Buba Galadima Ya yi ikirarin cewa mutane 440 cikin 470 da aka karrama ya kamata suna gidajen yari a sassan kasar a hiran da aka yi shi a Arise TV a ranar Juma’a 14 ga watan Oktoba.
An kara tsare Greenwood na Man United
Ya ce: “Idan ka ce Buba Galadima, ka yi amfani da Injiniya, Alhaji ko wani abu?
Ban taba karbar sarauta ba kuma ko Galadima, idan da yadda na so kuma ba don yana takardun karatu na daga frimare zuwa jami’a ba, da na cire kalmar (Galadima) don sarauta ce kuma bana bukata.
Bari in fada maka, cikin mutum 447 da aka bawa lambar yabo na kasa, ina tunanin 440 cikinsu kamata ya yi suna gidan yari a maimakon gabatar da su a matsayin wadanda suka cancani karramawa.
Menen dalilin karramawar? Wace karamci suke da shi? “Sakayya ne kawai ga yara kuma ka zan Muhammadu Buhari da kansa ya zargi Cif Olusegun Obasanjo, marigayi Musa Yar’Adua da Goodluck Jonathan ta bada lambar yabo, da karrama mutanen da akwai alamar tambaya a halayensu.”
Ya cigaba da cewa: “Wanene cikin wadanda aka bawa lambar yabon ke da halin kirki tas? a gani na, kamata ya yi a rika bada irin wannan lambar yabon ga mutanen da suka yi ritaya daga aiki kuma EFCC da ICPC ba su rika binsu ba.
“Kazalika, a rika bawa wadanda suka mutu yayin yi wa kasarsu hidima.
Gara in bawa mai girki da ya iya dafa abinci maimakon mai sayar da katin waya da ya zama tiriloniya kuma wannan shine ra’ayi na.”
Dan siyasan ya kuma ce yana kyautata zaton dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa ta NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso zai yi nasara a zaben 2023, duba da irin ayyukan da ya yi matsayin ma’aikacin gwamnati.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
