News
Abin da ya sa na ƙi bayyana manufofina – Kwankwaso
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ɗantakarar shugaban ƙasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party a Najeriya ya ce ana ci gaba da tsare-tsare domin kafa kwamitin yaƙin neman zaɓensa.
Kwankwaso ya ce ya kuma jinkirta bayyana manufofinsa ne domin gudun ‘satar amsa’ daga sauran jam’iyyun siyasa na ƙasar.
Mutum miliyan huɗu ne suka ziyarci Ƙabarin Manzon Allah a cikin wata uku
Wasu dai na ganin Rabiu Musa Kwankwanso na jan-ƙafa wajen kafa kwamitin yayin da sauran jam’iyyu suka sanar da nasu tare da fara gangamin yaƙin neman zaɓen.
A cewarsa “za mu fito ne da tsari wanda ya banbanta da na sauran ƴan takara.”
Ya ƙara da cewa “Za mu fito da tsarin abin da za mu yi, da kuma yadda za mu aiwatar da shi.”
Ya ƙara da cewa ya shiga dukkanin manyan jam’iyyun ƙasar biyu (APC da PDP) amma ya dawo daga rakiyar su saboda sun gaza samar da manufofin da za su ciyar da ƙasar gaba.
Tarko aka kafa min a Kaduna’
Ɗan takaran na jam’iyyar NNPP ya kuma yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa ya ƙi amsa gayyatar ƙungiyoyin Arewa domin bayyana ƙudurorinsa ga yankin.
A cewar sa “…shi ya sa aka kafa tarko a Kaduna, suna so idan na je na yi bayani, daga baya su ce ga wani ɗan takara shi ya fi cancanta.”
Ƴan takaran shugaban ƙasa huɗu ne suka halarci tattaunawar, wadda gamayyar ƙungiyoyi masu kare muradun arewacin Najeriya suka shirya a gidan tsohon firaiministan yankin, Ahmadu Bello.
Ƙungiyoyin da suka shirya taron sun ce manufarsu ita ce su ji bayanai daga ƴan takara kan tanadin da suka yi wa yankin, sannan su faɗa wa ƴan takaran nasu buƙatun.
Kuma sun musanta duk wasu zarge-zargen cewa sun shirya taron ne domin nuna goyon baya ga wani ɗan takara.
BBC HAUSA
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
