News
ECOWAS Ta Bukuci A Gudanar Da Sahihin Zaben 2023 A Najeriya
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ta roki hukumomin Najeriya da su tashi tsaye, wajen ganin kasar ta gudanar da karbaben zabe a shekara mai zuwa saboda muhimmancin ta ga Afirka baki daya.
Tawagar kungiyar da ta ziyarci Najeriya domin ganin shirin zaben a karkashin tsohon shugabar hukumar zaben Ghana, Dr Kwadwo Afari-Gyan, ta bayyana haka ne lokacin da ta gana da shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmud Yakubu a birnin Abuja.
Sojoji sun tarwatsa masu zanga-zanga a Sudan
Shugaban bangaren siyasa na kungiyar ECOWAS, Dr Remi Ajibewa yace sun ziyarci Najeriya ne domin ganin yadda shirin zaben ke gudana kamar yadda dokar kungiyar ta tanada.
Ajibewa yace kudurorin kungiyar sashe na 11 da 12 da na 13 sun baiwa kungiyar damar tura jami’an sa ido kowacce kasa dake yankin duk lokacin da za’a gudanar da zaben shugaban kasa.
Saboda haka jami’in yace ziyarar da suka kai Najeriya ba itace ta farko ba, domin duk lokacin da za’a gudanar da zabe sukan yi haka.
Daraktan yace ECOWAS ta bayyana fatan ganin zaben na shekara mai zuwa ya gudana ba tare da matsala ba, saboda irin jagorancin da Najeriya ke bayarwa a yankin.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
