Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi taro da manyan hafsoshin tsaron ƙasar, ranar Litinin domin sake duba halin da tsaron ƙasar ke ciki.
A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan kafafen yada labarai Malam Garba shehu ya fitar, ya ce a yayin ganawar shugaban ƙasar zai saurari bayanai daga manyan hafsoshin tsaron, tare da ƙara ƙaimi a fannonin da ke buƙatar kulawa.
Rahama Sadau Ta Zama Gwarzuwar Finafinai Ta Afirka
A ‘yan kwanakin nan ne dai Ofisoshin jakadancin Amurka da na Birtaniya a Najeriya suka fitar da jerin gargaɗin cewa akwai barazanar kai hare-hare a wasu sasan ƙasar, har ma da Abuja.
