News
An tura jami’an tsaro domin ceto manoman da aka sace a Katsina
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumomi a Najeriya sun ce an tura jami’an tsaron ƙasar domin ceto mutane sama da 20 waɗanda ƴan bindiga suka sace a wata gona da ke jihar Katsina.
Cikin mutanen da aka sacen har da mata da dama.
Masu ruwa da tsakin APC na karamar hukumar Doguwa sun ziyarci Sulen Garo
Mazauna yankin da abin ya faru sun ce maharan sun zo ne da yawa a kan babura inda suka dirar wa masu girbin amfanin gona a kusa da ƙauyen Mairuwa da ke jihar.
Mai magana da yawun rundunar ƴansandan Najeriya a jihar ta Katsina ya shaida wa BBC cewa mutane 21 aka sace a lokacin harin wanda aka kai a ranar Lahadi.
Sai dai wasu bayanan na cewa yawan mutanen da aka sacen ya zarce haka.
Advertisements
