Sports
Chelsea da Man City na son dauko Leao, PSG na zawarcin Endrick
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Chelsea da Manchester City na son dauko mai kai harin Portugal kuma dan wasan AC Milan Rafael Leao, mai shekara 23, kan farashin fam miliyan 105. (Tutto Mercato via Mail)
Amma AC Milan na zakwadin bude sabon kwantiragi da Leao, wanda kwantiraginsa zai kare a kakar wasan 2024. (Calciomercato)
Real Madrid ta damu kan tuntubar da Liverpool ta yi wa Borussia Dortmund kan dan wasan tsakiya na Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, inda suke fatan zai zamo babban kamun da za su yi nan ba da jimawa ba. (Marca – in Spanish)
Paris St-Germain, da Chelsea da Real Madrid na zawarcin dan wasan tsakiya na Palmeiras da Manchester United Endrick. Dan Brazil din mai shekara 16 da ake yi wa lakabi da sabon Neymar ka iya barin kulub din shi kan farashin fam miliyan 55 da zarar ya cika shekra 18. (Fabrizio Romano via Sun)
Manchester United na sa ido kan mai kai harin Slovenia, Benjamin Sesko mai shekara 19, sai dai dan wasan na RB Salzburg ya fara tuntubar takwarar kungiyar shi wato RB Leipzig. (Telegraph)
Arsenal na tuntubar mai tsaron raga na Italiya Victoria Guimaraes kan farashin fam miliyan 26, Ibrahima Bamba, mai shekara 20 (Mirror)
Barcelona na duba yiwuwar dauko dan wasan baya na Sifaniya Jordi Alba, mai shekara 33 kuma jagoran Napoli. (El Nacional – in Spanish)
An cika akwatin sakonnin shafin Tiwita na kungiyar Arsenal, sakonnin kan su dauko dan wasan Leicester kuma na tsakiyar Youri Tielemans mai shekara 25 da ya zura kwallye a ragar Everton. (Express)
Erik ten Hag ya nuna sha’awar dauko dan wasan gaba na Serbia da Juventus Dusan Vlahovic, mai shekara 22, zuwa Old Trafford. (Sun)
