Connect with us

News

Wani mutum ya cinna wa dakin ‘ya’yan matarsa wuta

Published

on

Yan sanda

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

 

 

 

Rundunar ‘yan sanda a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya ta kama wani mutum bisa zargin kunnawa ‘ya’yan matarsa wuta.

Advertisement

 

Jami’in hulda da jama’a a rundunar ‘yan sandan jihar SP Funmilayo Odunlami ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran kasar faruwar lamarin a Akure babban birnin jihar.

Dala na gab da zarta Naira dubu a Najeriya.

Ya ce lamarin ya faru ne ranar Asabar, inda ya ce jami’an ‘yan sanda suna gudanar da bincike, yayin da yaran ke samun kulawar likitoci a babban asibitin Owo.

 

Ya kara da cewa an mayar da batun zuwa ga sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar, domin gudanar da bincike yadda ya kamata.

Advertisement

 

Wani shaida ya fada wa kamfanin dillacin labaran kasa NAN cewa mutumin ya kunna wuta a dakin da yaran ke kwance ne sakamakon samun ‘yar rashin jituwa da matar tasa.

 

Majiyar BBC kara da cewa daya daga cikin yaran ya rasa ransa, sakamakon wutar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending