Connect with us

News

Zan Rage Haraji, In Hako danyen mai a Borno —Atiku

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya alkawarin rage haraji da kuma hako danyen mai da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya da Tafkin Chadi idan ya ci zabe.

Advertisement

Dan takarar, yayin kaddamar da yakin neman zabensa na yankin Arewa maso Gabas, a Maiduguri, Jihar Borno, ya yi akawarin farfado da Tafkin Chadi, bukatar da ya ce, Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Garbai, ya yi.

Farashin litar fetur zai kai N410 idan aka janye tallafi, in ji NNPC

Advertisement

Aminiya ta rawaito cewa A jawabinsa ranar Laraba a Maidugri wadda ita ce cibiyar kungiyar Boko Haram, dan takarar ya yi alkawrin magance matsalar tsaron da ta addabi yankin da ma sauran yankunan Najeriya.

“Kafin zuwata nan na ziyarci Fadar Shehun Borno, kuma a jawabinsa ya bukaci mu magance wasu matsaloli hudu ko biyar da ke addabar Borno.

Advertisement

“Na farki shi ne dawo da tsaro da zaman lafiya a jihar kuma na yi masa alkawari cewa za mu yi, idan Allah Ya kai mu PDP ta ci zabe za a samu tsaro da aminci a Borno.

“Na biyu shi ne mu farfado da Tafkin Chadi domin manoma su koma gonakinsu su ci gaba da samar da abinci da ayyukan yi.

Advertisement

“Ya bukaci mu tabbata kananan hukumomi sun samu wutar lantarki, muka yi alkawarin yi.

“Haka kuma ya bukaci mu dawo da hakar danyen mai a yankin Tafkin Chadi, shi ma mun yi masa alakwarin da yardar Allah.”

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending