News
Mun Shirya Dakile Sayen Kadarori Da Kudaden Haram-Cewar Hukumar EFCC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta ce ta shirya tsaf domin dakile halatta kudin haram ta hanyar sayen kaddarori da kayan abinci da tsabar kudi domin kaucewa sabuwar dokar canja naira.
Jam’iyyar APC Ta Lashe Dukkan Zaben Kananan Hukumomin Neja Yayin Da PDP Ta Kauracewa Zabe
A hirarshi da Muryar Amurka, Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrashid Bawa, ya ce dokar kasa da ta hana halasta kudaden haram ta kuma kayyade cinikayya da mutum zai iya yi da kudi tsagoransu, idan mutum ya yi ciniki da ya wuce Naira miliyan biyar lokacin guda sai shine idan mutum ne, idan kuma kamfani ne Naira miliyan goma, duk wannan doka ta kasa tana nan.
Ya,ce Kuma zasuyi duk Mai yiwuwa wajen ganin an dagile wannan barakar dake addabar kasar,sa ta nigeria
