News
Osinbajo ya rera waka ‘Buga’, a wajen taro
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A ranar Talata ne mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya faranta wa mahalarta taron duniya yawon bude ido na Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar a garin Iganmu na jihar Legas a lokacin da ya ba da fassarar wakar Kizz Daniel mai taken “Buga”.
A wajen taron, wanda wakilinmu ya sanyawa ido ta gidan Talabijin na Channels, mataimakin shugaban kasar ya yi jawabi a kan taken taron, ‘Hade yawon bude ido, al’adu da masana’antu masu kirkire-kirkire: hanyoyin farfadowa da inganta ci gaba.
Kwararen Likita A Fannin Daya Shafi Kunne da Hanci da kuma Makogwaro, na farko a Jihar Kano ya rasu
Osinbajo ya shaida wa mahalarta taron, wadanda aka zabo daga sassa daban-daban na duniya, cewa waka harshe ce ta duniya da mutane za su ji dadin ba tare da fahimtar wakokin ba.
Ya ce, “Kiɗa, kamar yadda muka sani, harshe ne na duniya. Har ma wadanda ba su san ma’anar kalmomin waka ba suna jin dadin yadda ake zato. Wasu kuma suna gano ma’anar waƙoƙin, suna gano al’adu da ra’ayoyin da ke ƙarfafa su.
“Amma bari in gwada wannan ka’idar tawa, wato, cewa ba kwa buƙatar fahimtar kalmomin kowace waƙa don jin daɗinta kuma ku iya rera ta kuma hakika kiɗan yare ne na duniya.”
Don Tabbatar da maganar sa , farfesa ya rera waƙar Kizz Daniel ta ‘Buga’; wani aiki da ya haifar da sowa da tafi daga mahalarta taron.
Ya kuma bukaci jama’a da su kasance tare da shi a cikin shirinsa yayin da yake nuna rawar da ake takawa da wakar ta hanyar daga kafadarsa.
Bayan raye-rayen da ya yi, Osinbajo ya ce, “A yau, ana yin wakokin Nijeriya da harsuna daban-daban a duk duniya. Don haka mutane a duk faɗin duniya suna rawa don wannan waƙar ta Kizz Daniel, mai suna ‘Buga’.”
