News
Kwararen Likita A Fannin Daya Shafi Kunne da Hanci da kuma Makogwaro, na farko a Jihar Kano ya rasu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kwararen Likita A Fannin Daya Shafi Kunne da Hanci da kuma Makogwaro, na farko a Jihar Kano ya rasu mai suna Dr Ado Hamza Soron Dinki
A wani rubutu da fitaccen dan jarida Abdullahi Usman ya yi a dandalin ‘yan jarida na Kano, sakon ya zo kamar haka
“Cikin bakin ciki da alhini, mun samu labarin rasuwar abokinmu Dokta Ado Hamza Soron Dinki,
Kwararen Likita A Fannin kunne da Hanci da kuma Makogwaro na farko a jihar Kano.
Ya rasu jiya 14/10/2022 da misalin karfe 10:30 na dare kuma za’ayi sallar jana’izarsa a yau 15 ga watan Nuwamba da misalin karfe 10:00 na safe a Soron Dinki Qtrs Kano Municipal.
Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma saka masa da Aljannar Firdausi Ameeen”.
NIGERIA TRACKER ta kuma tabbatar da rasuwar Dr Soron Dinki daga majiya mai tushe a cikin al’ummar sa.
