Connect with us

News

Ba za mu sauya matsayinmu ba kan ASUU – Ministan Ilimi

Published

on

Adamu Adamu

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Yayin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ke gudanar da zanga-zangar lumana a faɗin jami’o’in ƙasar domin nuna rashin jin daɗinsu game da rashin biyansu albashin watannin da suka kwashe suna yajin aiki, gwamnatin ƙasar ta ce ba za ta biya malaman albashin aikin da ba su yi ba.

Advertisement

Mutum 412 ne suka mutu a hatsarin ababen hawa cikin wata 10 a Legas – FRSC

Ministan ilimin ƙasar Malam Adamu Adamu ne ya bayyana haka ranar Laraba bayan taron majalisar zartarwa da shugaban ƙasar ya jagoranta a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja babban birnin ƙasar.

Advertisement

Yayin da yake martani game da iƙirarin da shugaban ASUU ya yi na cewa gwamnati na son mayar da malaman jami’ar ma’aikatan wucin-gadi, ministan ya ce gwamnatin ba ta da wannan niyyar.

“An janye yajin aiki, kuma gwamnati ta biyasu haƙƙin iya aikin da suka yi. Ina tunani wannan shi ne matsayin gwamnati, cewa ba wanda za a biya albashin aikin da bai yi ba, sun yi aiki na kwanaki, kuma gwamnati ta biya su haƙƙinsu kwanakin da suka yi”, in ji Adamu Adamu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending