News
Babu abin da zai hana mu taimaka wa Ukraine – Sifaniya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ministar harkokin tsaron Sifaniya Margarita Robles ta ce babu wani tashin hankali da zai hana ƙasarta taimaka wa Ukraine.
Tana magana ne a yayin da aka gano wata takarda ƙunshe da bam a ƙasar wadda aka ƙwace a ofishin Jakadancin Amurka da ke Madrid.
Ms Margarita ke cewa ƴan sanda suna gudanar da bincike amma abin da ya zama dole a fayyace shi ne, babu wani tashin hankali da zai sauya ƙudirin Spaniya da ƙasashen Nato da Tarayyar Turai na goyon bayan Ukraine.
A ranar Laraba ne wata wasiƙa da aka aike wa jakadan Ukraine ta kama da wuta inda wani ma’aikaci a ofishin jakadancin ya ji rauni.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa wataƙila an aika wasiƙar ne daga cik in ƙasar.
Advertisements
