Connect with us

Business

NNPC Zai Samar Da N1tn Dan Gudanar Da Ayyukan Tituna  – Kyari

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Kamfanin man fetur na Najeriya zai samar da karin Naira tiriliyan 1tn don gudanar da ayyukan tituna a Najeriya, in ji shugaban rukunin kamfanin na NNPC, Mele Kyari.

 

Advertisement

Kyari ya bayyana hakan ne a Legas a ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba, yayin rangadin aikin gina titin Agbara-Badagry.

Wata sabuwa farashin litar man fetur ta kai N310 a wasu gidajen mai a jihar Kano.

Ya ce za a kashe Naira tiriliyan 1tn ne a kan ayyukan tituna ta hanyar tsarin biyan harajin ababen more rayuwa na gwamnatin tarayya

Advertisement

 

Jaridu sun rawaito cewa a kusan kwata na uku na shekarar 2021, kamfanin mai na kasa NNPC ya bayyana aniyarsa ta samar da kudade domin sake gina wasu zababbun ayyukan tituna domin saukaka zirga-zirgar albarkatun man fetur.

Advertisement

 

Kyari ya ce, “Mun yi matukar farin ciki da yadda wannan ci gaban hanyoyin ya kasance. Mun yi matukar farin ciki da wannan shiga tsakani a fadin kasar ba wai a wannan wuri kadai ba. Muna yin kilomita 1,800 a fadin kasar. Muna daukar wani sashe na sama da Naira tiriliyan 1tn na zuba jari a hanyoyin samar da ababen more rayuwa a kasar nan.

Advertisement

 

“Mun yi imanin cewa wannan tsarin bashi na haraji da shugaban kasa ya sanya shi ne kawo sauyi ga kasarmu.

Advertisement

 

“Mun yi imanin cewa nan da watanni 24 masu zuwa, za a samu gagarumin sauyi ga hanyoyin sadarwa a kasar nan baki daya kuma shi ya sa kamfanin NNPC ya zama kamfanin ku kuma yana yi mana aiki baki daya.

Advertisement

 

“Muna tunanin cewa ita ce hanya mafi kyau don shiga tsakani da kuma samar da ababen more rayuwa. Muna kara wani kudi, ba mu kai ga karshe ba, amma na san ya wuce Naira tiriliysn 1tn.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending