Connect with us

Business

Matakin G7 Na Karya Farashin Man Rasha Ya Fara Aiki

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Takunkumin da manyan kasashen duniya, (G7) suka kakaba na kayyade farashin danyen man da Rasha fitarwa ta teku a kan Dala 60 ta fara aiki.

 

Advertisement

Kasashen G7 da da Australiya da kasashe 27 na Tarayyar Turai (EU) sun sanya mizanin farashin da ya fara aiki a ranar Litinin ne da nufin hana Rasha samun kudaden daukar nauyin yakinta da Ukraine.

 

Advertisement

An wallafa hoton bizar Tinubu don nunawa ƴan adawa cewa Amurka ba ta hana shi shiga ba

Sun kuma haramta wa kamfanoni masu zaman kansu bai wa Rasha tankoin mai, idan ba za ta sayar da danyen man nata a Dala 60 ko kasa da haka ba.

 

Advertisement

Haka kuma an haramta ba su taimakon kudi ko wata hidima, idan farashin ya haura haka, idan ba a lokacin ibtila’i ko tsautsayi ba.

 

Advertisement

 

Duk jirgin wata kasa da ya dauki man Rasha a fiye da Dala 60 kuma za a haramta masa inshora da graya da samun kudade na tsawon kwana 90.

Advertisement

 

A cewarsu, hakan zai samar da daidaito a kasuwar danyen mai ta duniya tare da ba wa wasu kasashe damar sayen man Rasha da ke kan teku, idan ya kai ko ya gaza farashin da suka kayyade.

Advertisement

 

Bayan duk wata biyu za a sauya farashin, farawa daga tsakiyar watan Janairun 2023, domin tabbatar da farashin man Rasha ya yi kasa da akalla kashi 5 cikin 100 na farashin da Kungiyar Kasashe Masu Hako Mai ta Duniya (OPEC) ta kayyade.

Advertisement

 

Duk sauyin da za a yi sai ya samun amincewar daukacin kasashen EU 27 da Australiya da kuma kasashen G7.

Advertisement

 

 

Advertisement

Duk lokacin da aka kayyade farashi zai samu sassaucin kwana 90 domin tabbatar da cewa bai shafi jiragen ruwan da ke dauke da mai a kan teku kafin a yi karin ba.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending