Sports
Shugaba Macron zai halarci wasan Faransa da Morocco a Qatar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban Faransa Emmanuel Macro zai je Qatar a ranar Laraba domin halartar buga wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya tsakanin Faransa da Morocco, Ministan wasanni Amélie Oudéa-Castera ta tabbatar da haka a gidan rediyon Faransa a yau Lahadi.
Kungiyar kwallon kafar Faransa za ta faffata da kungiyar kwallon kafar Morocco ranar laraba a wasan daf da na karshe a gasar cin kofin Duniya da ke gudana a Qatar bayan nasarori da kungiyoyin suka samu ,Faransa ta lallasa Ingila da ci 2 da 1,yayinda Morocco dake wakiltar nahiyar Afrika,wanda shine karo na farko da Afirka ta kai wannan mataki ta doke Fotugal da ci 1 mai ban haushi duk da kasancewar tauraron Fotugal Christiano Ronaldo.
Tsananin Tashin Kayan Masarufi Nasa Wasu Magidanta Tsallake Cin Abincin Rana ko Na Safe
A birnin Paris na kasar Faransa zuwa wasu manyan birane na nahiyar Afrika da suka hada da Alkha’ira,Rabat ;Doha dubban magoya bayan Faransa da Morocco sun yi bikin tare.
Faransa ta rugumi yan kasar Morocco da dama inda wasu ke kallon wannan wasa tsakanin Faransa da Morocco tamkar wasa tsakanin mahaifi da mahaifiya kamar dai yadda akasarin yan Morocco suka sheidawa rediyon Faransa rfi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
