News
Mjalisa na son Emefiele ya yi mata bayani kan tsarin takaita cire kudi a bankuna
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Yan majalisar wakilan kasar sun fusata sakamakon gazawar da gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele ya yi wajen zuwan gaban su domin ya yi bayani a kan ka`idar takaita cire kudi daga asussan ajiya da babban bankin ya gicciya.
Wannan dai shi ne karo na biyu da gwamnan babban bankin yake kasa amsa gayyatar `yan majalisar. Sai majalisar ta tsayar da ranar Alhamis mai zuwa domin gurfana a gabanta.
Honarabul Abdullahi Mahmud Gaya dan majalisar ne mai wakiltar mazabar Gaya da Ajingi da Albasu daga jihar Kano, kuma a tattaunawarsa da Ibrahim Isa ya fada masa dalilin kiran da suka yi wa Emefiele.
Dalilin da ya sa muka kira gwamnan babban bankin Najeriya domin ya yi mana bayani kan batun takaita kudaden da mutum zai cira, yawanci ayyukan da gwamnati ta yi alkawarin yi ba ta yi ba, idan aka kawo batun nan mu za mu cutu.
Maganar gaskiya wasu daga cikin mazabunmu kamar ni da na fito daga Gaya da Ajingi, ba mu da banki ko daya, to ka ga anan akwai matsala kenan.
Idan mutane za su bude asusun ajiyar banki sai sun bar garuruwanmu zuwa cikin gari, saboda babban bankin Najeriya bai wa bankunanan ‘yan kasuwa damar bude rassa a irin wuraren ba,” in ji Honarabul Gaya.
Wannan batu na takaita kudin da masu asusun ajiyar banki za su cira ko su tura, da babban bankin Najeriya CBN ya bulla da shi, na ci gaba da daukar hankali da janyo muhawara da cece-kuce a Najeriya.
