News
NDLEA ta kama mutum 12 bisa zargin shigar da tabar wiwi Najeriya
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Jami’an Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya sun kama wata tabar wiwi da aka yi safararta daga ƙasashen waje a tashar jiragen ruwa ta Apapa da kuma filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke birnin Legas.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce ta samu tabar ƙunshe cikin wasu ababen hawa da aka shigo da su daga ƙasar Canada, da kuma wata da aka shigo da ita daga ƙasar Afirka ta Kudu.
Jami’an hukumar sun ce an shigo da ita ne domin sayar da ita, tare da yin amfani da ita a lokutan bukukuwan Kirsimeti.
Hukumar ta ce ta kama mutum 12 da take zargi suna da alaƙa da shigo da tabar.
Advertisements
