Connect with us

Sports

An saka wa jarirai 738 sunan Pele a Peru

Published

on

Pele

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Yayin da ake ci gaba da jana’izar shahararren dan kwallon Brazil da ma duniya baki daya wato Pele, hukumar da ke yi wa jarirai rajista a Peru ta ce iyaye 738 ne suka saka wa ya’yan da suka haifa sunan mamacin.

Advertisement

Tinubu Ya Fi Ni Lafiya, In Ji Kashim Shettima

Kamar yadda rajistar da ke dauke da sunayen ta nuna, an rika saka sunayen daban daban kamar Pele, King Pele, Edson Arantes, ko kuma Edson Arantes do Nascimento, wanda shi ne cikakken sunan na Pele.

Advertisement

Pele ya mutu ranar Alhamis, bayan fama da cutar kansa yana da shekaru 82.

Yanzu haka al’umma na ci gaba da jerin gwano a birnin Santos, don yin tozali da gawar ta Pele

Advertisement

A Santos ne Pele ya fara wasa tun yana matashi, kuma mafi yawan kwallayen da ya ci sama da 1000 a nan ne ya ci su.

Daga cikin masu ta’aziyar Pele akwai sabon Shugaban Brazil Lula da Silva, da kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino da ma wasu yan wasan Brazil

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending