Connect with us

News

Kotu Ta Yi Wa Matashi Bulala 5 Kan Satar Dabino A Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Jihar Kano, ta bayar da umarnin yi wa wani matashi mai suna Alkasim Murtala bulala biyar bisa laifin satar dabino kwano hudu.

Advertisement

 

Murtala mai shekaru 25 wanda ke zaune a unguwar Koki a Kano, an same shi da laifuka biyu da suka hada da keta haddi da kuma aikata sata.

Advertisement

Kotu Ta Soke Zaben Adekele A Matsayin Gwamnan Osun

Alkalin kotun, Malam Isma’il Muhammad Ahmed, ya yanke wa wanda ake kara hukuncin zaman gidan yari na wata daya ko biyan tarar Naira 5,000 tare da bulala biyar, bayan ya amsa laifinsa.

 

Advertisement

Tun da farko, lauyan masu kara, Abdullahi Wada, ya shaida wa kotun cewa wani Ahmed Malamai ne ya kai karar ofishin ‘yan sanda na Fagge da ke Kano a ranar 24 ga Janairu.

 

Advertisement

 

Ya ce wanda ake tuhumar ya kutsa cikin shagon Malamai da ke Kasuwar Sabon Gari, inda ya saci dabino kwano hudu wanda kudinsa ya kai Naira 10,000.

Advertisement

 

Wada, ya ce laifin ya ci karo da sashe na 133 dana  120 na Kundin Laifukan Shari’a na Jihar Kano.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending