News
Akwai Fargabar Rasa Rayuka Yayin Da Rikici Ya Kaure Tsakanin APC da NNPP a Kano
Ana zargin an kashe mutane tare da kona motoci tara a karamar hukumar Tudun Wada bayan da wani rikici ya kaure tsakanin magoya bayan jam’iyar APC da jam’iyar NNPP .
Tun da fari dai anyi zargin cewa magoya bayan NNPP ne suka shirya taron siyasa a ranar Lahadi inda kuma rikici ya kaure tsakanin su dana APC.
An kuma cigaba da zaman dardar yayin da jami’an tsaro ke kwantar da tarzoma a yankin.
Ko a ranar Alhamis ma dai irin wannan rikici ya kaure a unguwar Kutama, a karamar hukumar Gwarzo wanda akayi zargin cewa an kashe mutum daya tare da raunata mutane da dama.
Premier radio ta rawaito cewa An kuma kone daya daga cikin gidajen shugaban karamar hukumar ta Gwarzo kurmus.
Advertisements
