Connect with us

News

Ba Za Mu Lamunci Yaɗa Labaran Bogi Gabanin Babban Zaɓe Ba–Sojoji

Published

on

 

 

Advertisement

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ba za ta lamunci labaran bogi da ake yaɗawa da sunan jami’anta ba a shafukan sada zumunta.

 

Advertisement

Rundanar, a wani martani da ta mayar kan wasu rubuce-rubuce da ke yawo a shafukan sada zumunta, ta ce mutanen da ke kokarin haifar da ruɗani ke amfani da sunanta.

Akwai Fargabar Rasa Rayuka Yayin Da  Rikici Ya Kaure Tsakanin APC da NNPP a Kano 

Babban Jami’in sadarwa na kasa a rundunar, Brigediya Janar Tukur Gusau, ya ce tuni sun kaddamar da bincike domin hukunta wadanda suka kirkiri wannan labari.

Advertisement

 

An dai rinƙa yawo da wasu bayanai kan rundunar da ke cewa, wasu daga cikin manyan jami’anta sun gana da daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa domin kawo rudani kan zaben da ake shirin gudanarwa nan da kwanaki goma sha uku masu zuwa.

Advertisement

 

Brigediya Tukur ya ce a ranar Asabar suka soma ganin rubutun a shafukan sada zumunta, kuma suna zargi wani da ke ganin ba a yi masa daidai ba ne ya ke daukan nauyin yaɗa labaran.

Advertisement

 

Ya ce a wannan hali da ake ciki bai kamata a ɓata sunan rundunar tsaro ta Najeriya ba.Shiyasa suka fito suka nemi waɗanda ke yaɗa wannan batu na soja na tattauna da ‘yan siyasa, su fito su yi bayyani inda suka samu labarinsu.

Advertisement

 

“Muna kalubalantar masu yadawa zance su fito su fadi inda suka samu bayanansu.

Advertisement

“Sannan za a gayyaci mutane domin amsa tambayoyi. Saboda a wannan hali bai kamata a bata sunan rundunar sojin kasa ba.”

 

Advertisement

Mun yi ammana da tsarin mulkin dimokuraɗiya da dokokinta. Kuma zamu yaki duka bin da zai kawo wat sarin mulkin karan-tsaye.”

 

Advertisement

Brigediya Tukur ya ce, akwai tsiraru da ke kokarin amfani da rundunar sojan Najeriya domin kawo rudani, amma dai su na sanar da su cewa ba za su yi nasara ba.

Rundunar ta ce duk wani abu da zai kasance matsala ga mulkin dimokuradiya za su dakile shi.

Advertisement

 

Sannan ya ce hakkinsu ne kare dimokuraɗiya da ‘yancita, shiyasa ba zau lamunci duk mai kokarin haifar da tunzuri ba.

Advertisement

 

Ya ce shi ba zai faɗi sunan kowa a bakinsa ba, amma dai ana bincike domin hukunta duk masu laifi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending