News
Sojojin Nijeriya 30 sun yi hatsari a Maiduguri
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar sojin Nijeriya ta ce wasu sojojinta da ke yin sintiri a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar sun yi hatsari.
Wata sanarwa da gidan talabijin na kasar, NTA, ya wallafa da safiyar Alhamis, ta ambato rundunar soji na cewa “dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun yi hatsari a yayin da suke sintiri a Arewacin Borno.
Hukumar RMAFC ta musanta karin albashi ga Tinubu, Gwamnatoci da sauran su
Runduna ta 3 da rundunar MNJTF sun tabbatar da cewa a cikin sojoji 30 da suka gamu da hatsarin babu wanda ya mutu.”
Sanarwar ta kara da cewa yanzu haka sojoji bakwai da suka jikkata suna samun kulawa a asibitin 7 Div. da ke Maiduguri.
Advertisements
