News
Yadda Marasa Lafiya Ke Wahala A Asibitocin Kano Sakamakon Ƙarancin ‘Cash’
Matsalar ƙarancin kuɗi ta jefa marasa lafiya a jihar Kano cikin wahala.
Wani bincike da jaridar Daily Trust on Sunday ta gudanar ya gano cewa da yawa daga cikin asibitocin jihar Kano ba sa karɓar tsarin tura kuɗi ta banki, sun fi son a ba su kuɗi a hannu.
Binciken ya gano yadda asibitoci da yawa suka cika da marasa lafiya, inda kowa yake faɗin irin wahalar da yake sha.
Ba Za Mu Lamunci Yaɗa Labaran Bogi Gabanin Babban Zaɓe Ba–Sojoji
Wani mara lafiya, Musa Saidu, ya ce ya je asibiti tun misalin ƙarfe 6:00 na safe, amma bai iya ganin likita ba saboda rashin kuɗi a hannu.
“Matsalar netwok ce babbar matsala a nan. Suna da injin POS amma babu netwok, kuma ba ni da kuɗi a hannu ballai in biya. Ina jin jiki yanzu haka, amma ba yadda na iya sai dai in koma gida. Na ga mutane suna ta wuce ni akan layi saboda suna da kuɗi a hannu”, in ji shi.
“Tana fama ne da hawan jini kuma mun daɗe da zuwa nan. Asibitin da muke zuwa yana da nisa kuma ba mu da tabbas ko za su karɓi taransifa. Ba don wani ya tausaya mata ba komai zai iya faruwa, amma mun gode Allah. Abin da muke jira yanzu shi ne ganin likita”, in ji wata mata da ta kawo wata mara lafiya.
A Asibitin Kula da Masu Cutar Yoyon Fitsari na Abubakar Imam, an ga yadda marasa lafiya ke shan wahala sakamakon rashin kuɗi a hannu, saboda asibitin ba ya amfani da banki.
Daily Trust on Sunday ta gano cewa asibitin ya buɗe asusun ajiya da Bankin Polaris, amma akan samu matsaloli wajen tura kuɗi a ciki.
“Yana yi mana wahala a nan saboda ba mu taɓa buɗe asusun banki ba, kuɗi muke karɓa. Amma saboda ganin yadda mutane suka wahala a makon da ya gabata, hukumar gudanarwar asibiti ta kawo wani asusu, amma har yanzu mutane suna wahala. Babbar matsala ita ce ta netwok”, in ji wani ma’aikaci da ya buƙaci a sakaye sunansa.
A Asibitin Sir Sunusi, wani mara lafiya ya ba da labarin yadda wata mai ciki ta kusa haihuwa a ƙasa, abin da ya sa ‘yan uwanta suka garzaya da ita gida.
“Sun zo nan makon da ya gabata amma ba su da kuɗin da za su biya asibiti. Sun jira wani ya kawo musu kudi amma bai zo ba. Lokacin da ta fara nuna alamar haihuwa har jini ya fara zuba, sai suka garzaya da ita gida.
“Abubuwa da yawa irin wannan sun faru a ranar amma ba sa so mutane su sani. An ce wani mara lafiya ma ya mutu a nan”, in ji wata mara lafiya, Hassana Ibrahim.
Wani babban jami’i a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, AKTH, wanda ya nemi a sakaye sunansa ya ce: “Ba a ba ni izinin magana akan wannan batu ba, amma kusan yanayin duk haka yake a ko’ina. Ba mu da ingantaccen tsarin biyan kudi ta Intanet, mutane suna wahala”.
An yi ƙoƙarin jin ta bakin Kwamishinan Lafiya na Kano, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa, amma bai ce komai ba.
