News
muhimmancin shan ruwa ga lafiyar jiki
Ruwa wani abu ne tsururu mara launi da ke dauke da sinadaran hydrogen da oxygen.
Ruwa dai yana da muhimmanci ga rayuwar mutane. Shan ruwa mai yawa ko kuma zama ba tare da kishirwa ba, abu ne da yake nuna cikakkiyar lafiyar mutum.
Jikin dan adam zai iya kasancewa ba tare da abinci ba har na tsawon makonni, amma hakan ba zai yiwu idan babu ruwa.
Hakan ya kara tabbata ne ganin cewa jikin ɗan adam na ɗauke da kashi 60 na ruwa, inda rashin ruwan kan shafi yanayin lafiyar jiki da kuma ta kwakwalwa.
Rashin shan ruwa, zai iya ƙara barazanar kamuwa da ciwon koda ga wasu mutane.
Bincike ya kuma nuna cewa shan isasshen ruwa, kan iya rage barazanar kamuwa da cutukan mara da kuma zafi yayin fitsari ga mata
Advertisements
