Connect with us

News

Kotu Ta Yanke Wa Mutum 2 Hukuncin Rataya A Kano

Published

on

 

 

Advertisement

Babban Kotun Jihar Kano mai lamba biyu ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same su da laifin kisan kai.

 

Advertisement

Kotun, wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a yusuf Ubale, ta sami Samaila Salisu da kuma Aminu Salisu da laifin kashe wani mai suna Ibrahim Alhassan.

Bayan sace ’yan mata 2 a jami’a, an fara gadin da kunan kwanan dalibai a Zamfara

Advertisement

Kotu ta yankewa Zakara hukuncin kisa a KANO

 

Sun shiga gidan marigayin ne da nufin aikata fashi da makami, inda a kokarinsu na yin haka, suka harbe shi.

Advertisement

An dai tuhume su ne da aikata hadin baki, kisan kai da kuma tayar da zaune tsaye, laifukan da kotun ta ce sun saba da sassa na 97, 221 (B) da na 114 na kundin Penal Code. Sai dai sun musanta aikata laifukan.

 

Advertisement

Lauyan masu shigar da kara, Barista Bashir Saleh, ya gabatar da shaidu har guda tara, ciki har da wasu ganau su uku, da kuma wasu hujjoji guda tara, ciki har da wata bindiga da kuma adda.

 

Advertisement

Bayan sauraron shaidu da hujjojin da aka gabatar, alkalin ya ce kotun ta gamsu da su.

 

Advertisement

Daga nan ne ya yanke wa mutum biyun hukuncin kisa ta hanyar rataya, sannan ya kara musu da daurin wata shida ko biyan tarar Naira 200,000.

Haka zalika, bisa samun su da laifin tayar da hankalin jama’a, kotun ta kara musu da karin hukuncin daurin shekara daya ko biyan tarar Naira 20,000.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending