News
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya Ta Fi Kowace Ƙasa Arhar Wutar Lantarki a Duniya
Ministan wutar lantaki Abubakar Aliyu ya ce Najeriya ta fi kowace ƙasa a duniya arhar kuɗin wutar lantarki
Ministan ya koka kan yadda ma’aikatu ke ƙin biyan kuɗin wutar lantarkin da su ke sha akan kari Kwamitin wuta ya shawarci ma’aikatar kuɗi ta riƙa cire kuɗin wutar daga asusun ma’aikatun da su ka ƙi biya
Ministan ya dai yi wannan jawabi ne jiya a Abuja a yayin wata tattaunawa da kwamitin wutar lantaki na majalisar dattawa, tare da kuma shuwagabannin wasu ɓangarori na hukumomin wutar lantarkin kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
Ya kuma ce duk da wannan garaɓasar da wutar ta ke da ita da kuma irin ƙoƙarin da gwamnati ta ke yi na ganin wutar ta wadaci ‘yan Najeriya, mutane da dama ciki harda wasu manyan ma’aikatun gwamnati ba sa son biyan kuɗin wutar.
Najeriya ta fi Nijar, Benin, Mali da Senegal arhar wuta Ya kuma ƙara da cewa a duk duniya babu waɗanda su ka kai ‘yan Najeriya shan wuta da arha, musamman in aka yi la’akari da irin kuɗaɗen da ake kashewa akan gas don samar da wutar lantaki
