Connect with us

Business

Kungiyar OPEC za ta yi taro don duba yiwuwar rage yawan man da take fitarwa

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZHRADEEN

 

Advertisement

Ƙungiyar ƙasashe Masu Arzikin Man Fetur ta OPEC za ta gudanar da taro a yau Lahadi tare da ƙawayenta domin tattauna batun rage yawan man da ƙungiyar ke fitarawa zuwa kasuwannin duniya.

kungiyar  ta shirya taron ne a daidai lokacin da farashin man ke faɗuwa a kasuwannin duniya sakamon matsin tattalin arziki da mafiya yawan ƙasashen duniya ke fuskanta, lamarin da ya haifar da rage yawan buƙatar man a ƙasashen.

Advertisement

Ministocin ƙasashe mambobin ƙungiyar 13 tare da ƙawayenta da Rasha za su gana a shalkwatar ƙungiyar da ke birnin Vienna domin tattaunawa game da batun.

A watan Afrilun da ya gabata ne ƙungiyar ta rage adadin man da take fitarwa zuwa kasuwannin duniya a wani mataki na farfado da farashin man a kasuwannain duniya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending