News
An kama wani malamin Jami’a yana sace wa ɗalibai waya a Aji
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An kama malamin Jami’a yana sace wa ɗalibai waya a Aji lokacin jarrabawa
Jaridar gaskiya tafi kwabo ta rawaito cewa, mutumin wanda ya ke sanye da rigar kwat da laktatyi, ya fara bin jakunan ɗalibai ɗaya bayan ɗaya yana ƙwashe wayoyinsa lokacin da suke tsaka da rubuta jarrabawa.
Yan Majallisar Dokokin Jihar Kano Zasu Karbi Horon Sanin Makamar Aiki
Sai dai hukumomi a jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile Ife a jihar Osun, wanda nan ne wannan lamari ya faru, sun musanta zargin cewa mutumin lakcara ne a makarantar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jami’ar Mr. Abiodun Olanrewaju ya fitar a ranar Laraba, ta ce, sam babu kamshin gaskiya cikin zancen.
“Eh gaskiya an kama wani mutum a aji yana sacewa ɗalibai wayoyi a jakarsu lokacin da suke tsaka da rubuta jarrabawa, amma a gaskiya wannan mutumin ba malami bane a jami’ar mu, kuma ba ɗalibi bane” inji Mista Abiodun.
“Muna zaton wani ɗan iskan gari ne ya shigo da shiga ta kamala ya aika ta wannan laifi , amma mu dai munsan ba malami ne shi a wannan jami’ar ba” inji shi
